Wednesday, 6 November 2019

Champions League:Chelsea da Ajax sun buga 4-4 wasan ya dauki hankula sosai

Wasan da aka buga tsakanin Chelsea Da Ajax na gasar cin kofin Champions League a daren jiya ya dauki hankula sosai. Tammy Abraham ne ya fara cin kungiyarshi ta Chelse bisa kuskure saidaoi Chelsea ta farke kwallon ta hannun Jorginho inda kuma Promes da ya ciwa Ajax kwallo ta 2.Wani bugun tazara da dan wasan Ajax, Ziyech ya buga ta taba hannun golan Chelsea ta shiga raga shine ci na 3 da akawa Chelsea kamin tagiya hutun rabin lokaci kuma cin ya dauki hankula sosai.

Ajax ta kara kwallo ta 4 bayan dawowa hutun rabin lokaci amma saidai kash ta samu jan kati har kuda biyu.

Bayan hakane Jorginho ya kara kwallo sannan James ya ci ta biyu wada wasan ya koma 4-4. Chelsea ta ci kwallo ta 5 amma aka kasheta.

Wannan shine karo na farko da aka taba cin Chelsea kwallaye 3 a gasar Champions League kamin a tafi hutun rabin lokaci, sannan shine karo na 2 tun bayan shekarar 2005 tsakanin Liverpool da AC Milan da aka ci wata kungiyar Ingila kwallaye 3 amma ta dawo duk ta ramasu a gasar Champions League.

Kwallon da Ziyech ya bayar aka ci Chelsea kwallo ta biyu ta dauki hankula sosai.Hakanan itama kwallon dan Ziyech din ya buga daga tazara me bisa ta taba hannun Golan Chelsea ta shiga raga ta dauki hankula.

Kwallon da dan wasan baya na Chelsea Zouma ya jawo tiryan-tiryan kamar zai yi abin arziki amma ya durmata sama itama ta dauki hankula sosai inda akai ta mai ba'a.


Valencia ta wa Lille ci 4-1 a dayan wasan na rukunin H
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment