Thursday, 7 November 2019

Champions League:Real Madrid, Juventus da PSG sun kai matakin kungiyoyi 16

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lallasa Galatasary da ci daidai har 6-0 a wasan da suka buga a daren jiya na gasar Champions League wanda wannan nasara ta baiwa Madrid din damar zuwa matakin kungiyoyi 16 a gasar na kifa daya kwala.
Matashin dan wasan Real Madrid, Rodrygo ne ya fara cin kwallaye 2 cikin mintuna 7 kacal da fara wasa wanda kuma sune kwallayen da aka ci cikin mafi kankanin lokaci a gasar.

Rodrygo ya samu damar kafa tarihin cin kwallaye 3 a wasa daya cikin makmfi kankanin lokaci a gasar bayan da Madrid ta samu bugun daga kai sai Gola amma Ramos wanda dama can shine ke bugawa Madrid irin wannan kwallo ya bugata kuma yaci.

Saidai da dama sun caccaki Ramos din inda sukace da ya baiwa matashin dan wasan damar kafa tarihin da babu irinshi.

Bensema ya ci kwallo wadda ta zama itace ta 50 da ya ci a gasar, kwallaye 2 yaci a jiyan. Sannan Rodrygo ya kara kwallo 1 wadda ta zama kwallonshi ta 3, ya kafa tarihin zama dan kwallon Madrid na biyu bayan Raul mafi karancin shekaru da ya ci kwallaye 3 a wasa daya na gasar Champions League.

Shima Benzema ya zama dan kwallo na 2 a gasar ta Champions League, bayan Messi, da ya jera kakar gasar 15 yana cin kwallaye a kowacce.

PSG ma ta kai matakin kungiyoyi 16 na gasar bayan lallasa Club Brugge da ta yi da ci 1-0

Bayern Munich ma ta kai matakin kungiyoyi 16 bayan doke Olympiacos da ci 2-0, Tottenham ta wa Red Star Hukunci da kwlalaye 4-0 wada biyu daga cikinsu Son ne ya ci mata, Tottenham na da wasa 1 da zata buga da Olympiacos wanda idan ta cishi to zata kai mataki na kungiyoyi 16.

Juventus ta kai matakin kungiyoyi 16 bayan lallasa Lokomotiv Moscow da ci 2-1 sai kuma wasan da Bayer Leverkusen ta wa Atletico Madrid ci 2-1.

Man City ta buga 1-1 da Atalanta duk da cewa an kashe kwallon da Jesus ya ci mata sannan ta kare wasan da 'yan kwallo 10 bayan samun jan kati.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment