Friday, 8 November 2019

China Ta Dauki Tsatstsauran Mataki Kan Yara Da Suke Buga Wasan Bidiyo

China ta kirkiro wani sabon tsari na takaita tsawon lokacin da kananan yara za su rika yi suna wasan wasa kwakwalwa da ake kira Video Games a harshen ingilishi.


Hukumomin kasar sun jima suna dora laifi akan yawan mu’amulla da video game da yaran kasar ke yi, a matsayin abin da ke kashewa yara karfin ido ya kuma sa su fadi a jarabawa a makaranta.

Daga yanzu, duk yaron da bai kai shekaru 18 ba, ba zai rika buga wasan na video game ba daga karfe goman-dare zuwa takwas na safe agogon yankin, sannan minti casa’in kawai za su rika yi kullum a tsakanin ranakun Litinin zuwa Juma’a, sannan a karshen mako da ranar da ake hutu, za su rika wasan na tsawon sa’o’i uku ne kawai.

China dai na daya daga cikin kasashen da kasuwar wasanni video game ke ja a duniya, inda ta kan samu kudaden shiga har dalar Amurka biliyan 33 a duk shekara.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment