Sunday, 3 November 2019

Da Najeriya zata kulle iyakokinta na tsawon shekaru 2 da laifuka sun ragu>>Gwamnan Babban bankin Najeriya

Shugaban babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa da Najeriya zata rufe iyakokinta na tsawon shekaru 2 da babu makawa laifuka zasu ragu a kasarnan.Yayi wannan maganane a wajan taron yaye daliban jami'ar Edo ranar Juma'ar data gabata.

Ya bayyana cewa da Najeriya zata zata rufe iyakokinta na tsawon shekaru 2 da laifuka irinsu zambar Yanar Gizo, Satar mutane dan kudin fansa, Fashi da makami dadai sauransu sun ragu sosai inda yace hakan zaisa dole mutane a koma Gona.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment