Tuesday, 5 November 2019

Dan Cristiano Ronaldo ya kama hanyar gadonshi inda yaci kwallaye 58

Masu iya magana kance, Barewa ba za tai gudu ba danta yayi rarrafe, hakanan,Kyan da ya gaji Ubansa, Abin ke shirin faruwa kenan da dan tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo.Dan na Ronaldo wanda ake wa lakabi da Ronaldo jr yana wasane a kungiyar kwallon kafa ta yara 'yan kasa da shekaru 9 na Juventus kuma ya fara kama kafar mahaifinshi wajan ci  kwallaye.

A yanzu dai Dan na Ronaldo ya ciwa Juventus kwallaye har 58 a wasanni 28 sannan kuma a shekarar nan da muke ciki ya bayar da taimako an ci kwallaye 18.

Wannan bajinta dan dan Na Ronaldo me shekaru 9 yayi tasa masu sharhi ke ganin cewa zai iya gadar uban nashi a kwallon kafa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment