Friday, 1 November 2019

DON ALLAH KARANTA WANNAN LABARIN ZAI ZAMA DARASI A GARE KA

Kwanaki biyu da suka gabata, na je wata unguwa dake wajen birnin Kano, na je duba lafiyar wani rarraunan Bawan Allah.

Bayan na fito, sai na yi sha'awar na fito titi da kafata, kafin na hau mota, da yake gidan yana cikin lungu, a daddafe na dinga bi ta cikin gonaki da kuma sabbin gidaje da ake gini, ina tafe ina ta tunanin rayuwa.


Kwatsam sai na ga wani katon saurayi yana rike da hannun wata karamar budurwar yarinya yana lugwuiguitawa, da alama yana jin dadin hakan ne.

A gefe kuma ga kayan tallanta nan alala da manja, yana kallo na ya saki hannun ta, na je gare shi na tsoratar da shi tare da cin zarafin sa, karshe dai guduwa ya yi ya cika wandonsa da iska, na so na bi shi, sai na ji tsoro saboda ban san shirin sa ba. Kuma gashi ban san kan garin ba.

Yarinyar ta razana kwarai da gaske, kuma Wallahi daga ganin ta ka san ba halinta bane,
na ce mata kada ta damu mu je ta nuna min gidansu, ta ce mun don Allah kada na fada a gidansu, na ce mata Wallahi ba zan fada ba.

Muka tafi har cikin gidansu, na sami mahaifiyarta mace mai hakuri da kamun kai, amman daga ganin ta talauci da babu sun ci karfin ta kuma daga ganin su babu mai agaza musu sai Allah.

Na tambaye ta ina mahaifin yarinyar nan?
Cikin yanayin ban tausayi ta ce shekarar sa tara da rasuwa, na ce mata me ya sa take dorawa wannan yarinyar talla?

Ta ce mun Wallahi sai an yi tallan ake samun na abinci, sai an yi tallan suke samun sukuni, ta ce ita kanta ba ta son tallar, amman ya zama dole saboda idan bikin yarinyar ya zo waye zai agazawa rayuwarsu? Waye zai yi mata kayan daki?

Cikin tausayi na ce mata Allah ne zai yi mata.
Na ce mata zan ba ta tallafi ta dinga yin sana'o'in su na mata a gida, sannan zan daukewa yarinyar kudin makaranta, tun daga yau din nan har izuwa ranar aurenta. Kuma kada ta damu da karfin ikon Allah, idan bikin ya zo, akwai kungiyar da na kafa mai suna 'MU TAIMAKI KANMU DA KANMU', za mu yi kokarin yi mata kayan daki irin yadda ake yi wa kowacce 'ya da take da rayayyen uba.

Ta fi minti biyu tana kuka, ta lissafo min dukkan abubuwan da za ta iya siyarwa a gida wanda ribar za ta ishe su, su dinga cin abinci har su ajiye wani abu, sannan na yi mata alkawarin duk lokacin da wata bukata ta taso ta kira ni, ni mai karamin karfi ne amma wallahi na  san Allah ba zai ba ni kunya ba .

Ina da wani muhimman abu da nake tattalin sa, tilas tasa na je na siyar da shi washe gari ma na je na yo mata dukkan siyayyar kayan, na tattara musu ragowar canjin na ba su saboda halin yau da gobe, mun rabu da su ina kuka su ma suna kuka, tare da alkawarin ba za ta taba sanar da wani cewar nine nayi mata haka ba.

 Karshe ma ce mata na yi a jihar Kaduna nake.

Mun rabu fuskokinsu cike da hawayen farin ciki tare da murnar sun sami wata sabuwar rayuwa.

Ni ba maraya bane, amna na san halin da marayu suke ciki, saboda gida na ko kasuwa bana rabo da su, bana nesa da su, duk sanda suka zo gidana da bukatar maraya hankali na kan tashi, nakan dimauce, ko ba ni da shi nakan ciwo bashi na yi musu, saboda ka kyautatawa dukkan wanda ya kawo kukan sa gare ka, saboda dubunnan mutane ya tsallake ya taho gare ka, to ka daure ka rufa masa asiri. Musamman ma marayan da ya rasa wanda zai agazawa rayuwarsa.

DARASIN DAKE CIKIN WANNAN JAWABIN

Shin me kake tunani idan wannan yarinyar ta ci gaba da talla marasa tsoron Allah suna shashashafa jikinta? Shin waye ya san irin rayuwar da za ta fada nan gaba da a ce ban je gare su ba?

Don Allah irin wadannan marayun suna da yawa a cikin unguwanninmu, wasu ma matsalar su ta fi ta wannan yarinyar. Marayu da dama suna shiga cikin kunci da masifar rayuwa saboda rashin wanda zai agaza musu.

Da yawan marayu sukan rasa sutura ko abinci, ko makwanci ko makaranta ko lalurar asibiti, sun rasa wanda zai agazawa rayuwarsu.

Da yawan marayu suna shiga karuwanci ko shaye-shaye, ko daba da ta'addanci saboda rashin wanda zai agazawa rayuwarsu. Muna da hannu wurin watsewar su, saboda da yawan mu ba ma agaxawa rayuwarsu, da yawanmu mun kauda kanmu daga gare su, kalilan ne daga cikinmu suke tallafawa rayuwarsu.

Muna kallon marayu a unguwanninmu, ba sa zuwa makaranta, ba su da abinci, ba su da sutura, ba su da mai agaza musu. Amma mun kauda kanmu saboda ba mu ne muka haife su ba, saboda ba 'ya'yan 'yan uwanmu bane. Kada mu manta fa da cewar maraicin nan ba siya suka yi ba, ba da son ransu suka rasa iyayen su ba, ba dan sun so ba suka rasa iyayensu.

Don Girman zatin Allah mu koma unguwanninmu mu binciko marayun da suka rasa iyayen su mu agazawa rayuwarsu. Wallahil Azeem ubangiji zai dube mu muma koda bayan rayuwarmu ne. Mu tuna da cewar wata rana muma za mu mutu, za mu rasu mu bar 'ya'yanmu ba mu da tabbas din yadda rayuwar su za ta fada. Wallahi duk mutumin da zai dinga agazawa marayu tabbas zai ga farin cikin rayuwa tare da nasarori.

Tallafawa marayu na sanyawa mutum farin ciki da nishadi a rayuwarsa, kuma babu mamaki wata rana wannan marayan da ka agazawa shine zai agazawa rayuwarka a lokacin daka gaza.

Da a ce za mu dinga duba marayun unguwarmu, mu dinga tallafawa rayuwarsu da mun samu babban cigaba a cikin alummarmu.

Maraici yana da matukar zafi da kuma taba zuciya.
Don Allah kaje ka tambayi wani maraya game da halin rayuwar da yake ciki wallahi karshe idan ba a yi wasa ba ka zubar da hawaye saboda tausayi.

Ka jarraba siya musu omon wanki ko sabulun wanka, ko garin kwaki ko kuma ka ba su abinci wallahi da sannu ubangiji zai daukaka matsayinka.

Da sannu za ka yi ta ganin nasara a rayuwarka.
Da a ce za mu dinga lura da su muna agazawa rayuwarsu da tuni mun wuce tarin matsaloli masu yawan gaske.

Ya Allah ka sanya farin ciki da nishadi a cikin rayuwar dukkan mutumin da yake agazawa maraya. Allah ka daukaka matsayin sa ka yalwata arzikin sa ka kyautata farko da karshensa, don matsayin Annabi Muhammadu SAW. Allah ka ba mu ikon agazawa rayuwar marayu.
Naku akoda yaushe.
SANI ROGO AIKAWA DALA KANO.
08082744019.WATHOP
09039128518.
08189582091.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment