Monday, 4 November 2019

Duniyar kwallo ta Kadu da ciwon da dan wasan Everton, Andre Gomez ya ji

Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Everton wasa, Andre Gomez ya ji mummunan raunin daya daga hankalin Duniyar kwallon kafa. Ya ji rauninne a wasan da syka buga da Tottenham a jiya Lahadi wanda ya kare da sakamakon 1-1.Dan wasan Tottenham,Son Heung-Min ne yayiwa Gomez amma ba da gangan ba.

Alkalin wasa ya baiwa Son katin Gardadi amma daga baya da ya ga irin ciwon da Gomez ya samu sai ya baiwa Son jan kati.


Gomez ya samu gocewar kashi a Agararshi da kuma karaya wanda kuma bayan likitoci masu bada taimakon gaggawa sun dubashi a filin wasan, an garzaya dashi Asibiti.

Raunin na Gomez ya tada hankulan 'yan wasan Tottenham da Everton din inda aka ga da yawansu na dora hannu a kai bayan da suka ga raunin nashi. Shi kanshi Son da dalilinshi Gomez ya ji raunin kuka kawai yayi ta yi da hakan ke nuna alamar bai ji dadi abin ba.Bayan kammala wasan, 'yan wasan Everton sun bi Son har dakin canja kaya inda suka rarrasheshi da nuna mai ba laifinshi bane kaddarace.

An kuma samu rahoton wani me goyon bayan Everton ya yiwa Son wanda dan kasar Koriya ta Kudune zagin wariyar launin fata. Everton din ta bayyana cewa tana kan binciken wannan lamari dan bata goyon bayan wariyar launin fata.


Wasi rahotanni sun bayyana cewa 'yan kallo da dama sun zubarwa Gomez da hawaye saboda ganin irin raunin da ya samu, wani kuwa har kusan shidewa yayi ya suma saboda ciwon na Gomez da ya gani.

Abokin wasan Gomez, Cenk Tosun da shine ya ciwa Everton kwallonta ya bayyana cewa da abinda ya faru da Gomez gara ace ma be ci kwallon ba, gara ace sun yi rashin nasara da ci 5-0.

Everton din, da tsohuwar kungiyar Gomez, Barcelona da Real Betis da Tottenham din duk sun aikewa da Gomez sakon jaje.

Everton ta bayyana cewa a Yau Litinin za'a wa Gomez aikin kafar tashiKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment