Saturday, 9 November 2019

Fadar gwamnatin tarayya ta tabbatar da sallamar Hadiman mataimakin shugaban kasa,Osinbajo

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa akwai gyare-gyaren da ake wa fadar shugaban kasa wanda kuma rage yawan ma'ikata da suka da ayyuka masu kamanceceniya na ciki wanda ya shafi wasu hadiman shugaban kasa dana mataimakin shugaban kasa.
Sanarwar da me magana da yawun shugaban kasa,Malam Garba Shehu ya fitar ta bayyana cewa canje-canjen da aka yi an yi sune da rage yawan kudin da ake kashewa wajan gudanar da ayyukan gwamnati da kuma kyautata ayyukan.

Sannan an lura akwai wasu hadiman shugaban kasa a zangon mulkinshi na farko da basu dawo a zangon mulkinshi na biyu ba.

Dan hakane aka dauki irin wannan gyara akan hadiman mataimakin shugaban kasa, ya kara da cewa, kuma bisa Al'ada mataimakin shugaban kasa ya fi shugaban kasa yawan hadimai kuma tuni dama ake son gyara wannan abu.

Yace wasu dake amfani da wannan dama suna cewa akwai matsala tsakanin shugaban kasa da mataimakinshi ba gaskiya bane, shugabannin kawunansu a hade suke kuma tare zasu kai Najeriya ga ci.

Babu wanda ya fi karfin shugaban kasa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment