Sunday, 3 November 2019

Fati Washa, Rahama Sadau da Ali Nuhu sun samu karramawa a kasar Ingila


Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Fatima Abdullahi da ake kira Fati Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka da aka gudanar a Birtaniya.


An sanar da Washa ne a matsayin gwarzuwar jaruma a taron karrama 'yan Fim da aka gudanar ranar Asabar a birnin London.

Bikin wanda ake kira Afro Hollywood Awards ya shafi karrama jaruman fina-finan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka,

Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din 'Sadauki.'

Jarumar ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a Fim din da ta fito "Jamila" da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a "Uwar Gulma"

Rahama Sadau ta wallafa hoton bidiyo a shafinta na Instagram, lokacin da Washa ta ke karbar kyautar, inda ta bayyana farin cikinta da godiya.

Hakanan Itama Rahama Sadau ta samu karramawa a matsayin jaruma ta musamman a wajan bayar da kyautar inda ta bayyana cewa tana godiya ga masoyanta.

Ali Nuhu ya samu kyautar gwarzon me bayar da umarni sai kuma Jamilu Ahmad Yakasai da shima ya samu kyautar karramawa.

Muna tayasu duka murna

Kalli bidiyon bayan da kyautar a kasa:

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment