Thursday, 7 November 2019

'Gidan mari ne ya fi dacewa da dana saboda gagararsa'

Wata mata da ke birnin Kano wadda na daga cikin iyayen da 'ya'yansu da aka kange a gidajen mari a fadin jihar, ta ce ba ta ji dadin yadda aka fasa gidajen marin ba.


Matar dai ta ce kasancewar dan nata 'gagararre' sannan kuma ita da mahifinsa duk sun tsufa ya sa ba ta fatan dan nata ya koma gida.

Gwamnatin jihar Kano dai ta bayar da umarni ga dukkan masu gidajen gidan mari da su kulle gidajen.

To sai dai da dama daga cikin mahaifan yaran ba su je sun dauki 'ya'yan nasu ba saboda tsoron abin da ka je ya zo.


Ranar Alhamis din ne dai rana ta karshe da gwamnatin jihar ta Kano ta bayar domin kowane mahaifi ya dauke dansa daga gidan marin.
BBChausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment