Thursday, 28 November 2019

Gidauniyar Jaruma Rashida Mai Sa'a Ta Ziyarci Sarkin Bichi

Hajiya Ambasada Rashida Adam Abdullahi Mai Sa'a, tsohuwar mataimakiyar mai girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin da ya shafi mata kuma Shugabar katafariyar Gidauniyar nan mai taimakon al'umma wato 'MAI SA'A CHARITY FOUNDATION', yau ma kamar yadda ta saba a ziyarce-ziyarcen manyan mutane masu daraja da take yi, ta kai ziyarar girmamawa ga Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero a jiya a fadar sa dake karamar hukumar Bichi.
Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna jin dadin sa kan ziyarar da Gidauniyar ta kai masa. Kuma ya yabawa shugabar Gidauniyar Hajiya Ambasada Rashida Adam Mai Sa'a, bisa namijin kokarin ta da tausayawar da take nunawa gajiyayyu, marassa karfi, 'yan gudun hijira, marayu da yara kanana marasa gata a fadin kasar nan.


Daga karshe Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi addu'ar Allah Ya yi wa Shugabar Gidauniyar albarka a dukkan lamuranta. Ya saka mata da gidan aljanna.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment