Friday, 1 November 2019

Gwamnan Kano ya saka hukuncin kisa kan masu garkuwa da Mutane

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya saka hukuncin kisa kan masu aikata laifin satar mutane dan neman kudin fansa, gwamnan a jiya, Alhamis ya bukaci ma'aikatqr shari'a ta jihar data yi gyaran da ya kamata dan tabbatar da wannan doka.
Gwamnan ya bayyana hakane a wajan kaddamar da kwamitin binciken yanda aka sace wasu yara da Kanon zuwa yankin Inyamurai.

Gwamnan ya bayyanawa kwamitin binciken me membobi 16 cewa yana da nan da wata 1 domin kammalawa da mika rahoto akan aikin nashi inda ya bayyana garkuwa da mutane a matsayin babban laifin da ya sabawa addinan kasarnan.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment