Sunday, 3 November 2019

Gwamnatin Saudiyya Na Tsare Da Wani Dan Nijeriya Tsawon Shekaru Biyu Ba Tare Da Laifin Komai Ba

SAKO GA GWAMNATIN NIJERIYA

Ni sunana, Ibrahim Ibrahim Abubakar Ibrahim zawiyya Gusau, jihar Zamfara.

Wato abun da ya faru Da ni, Ni dai na zo nan kasar Saudiyya ne, domin gudanar da ibadar Ummura. Shekara biyu da rabi da suka gabata. Ina cikin wadanda Gwamnatin Jihar Zamfara ta wancan lokacin ta dauki nauyin zuwansu, Umrah. Karkashin jagorancin tsohon gwamna Abdul-Aziz Yari. 


Mun taso ne daga filin jirgin Sama na Malam Aminu Kano, a cikin jirgin Ethiopia, Ranar wata juma'a 10-03-2017. Mun sauka a filin jirgin Sama, na Sarki Abdul-Aziz, da ke Jiddah, da Asubahin Ranar Asabar 11-03-2017, Mun kama hanyar mu zuwa Madina, Mun sauka Madina a wani otel da ake kira Badrul- Ambariyya. Mun je harami mun dawo har mun shiga bacci, kimanin karfe sha biyu na dare, sai mu ka ji ana kwankwasa kofar dakin mu, dama ba mu kulle dakin ba, saboda akwai wanda ya fita a cikinmu. 

Kawai sai mu ka ga wasu mutane a cikin fararen kaya, sun afka mana da karfin tsiya, suka kama mu suka rike, su ka yi ta binciken dakin da kuma jakunkunan mu, ba su ga komai ba da suka gama. Sai suka saka mani sarka, hannu da kafa suka tafi da ni. A hanya sai na ke tambayar su da larabci, mene ne laifi na aka kama ni suka ce su ma ba su sani ba, an dai ce ma su ne, su zo da ni. Har suke tambaya ta halan ina ta'ammuli da magunguna ko miyagun kwayoyi? Na ce ma su a'a. Daga nan sai suka kai ni ofishin 'yan sanda na garin Madina, sashen masu kula da miyagun kwayoyi. Bayan nan sai aka ce, a wuce Jeddah a nan ake nema na. 

Bayan kwana biyu, Sai aka mayar dani Jiddah, wurin ýan Sanda masu kula da miyagun kwayoyi. Bayan mako daya, Sai aka kaini wurin tambaya, aka dauko wani Bahaushe baki dogo kakkaura haka, a matsayin Wanda zai mani tafinta, Sai ya ce suna tuhumarka da shigowa da kwayoyin tramadol kimanin dubu daya da Dari hudu da tis'in da bakwai. (1,497)Sai na ce toh a ina aka same shi? Ni da an duba jakata ba a ga komai ba a cikinta, Sai sutura ta da Ihrami kadai, Sai suka ce eh ai ba a wurina aka same su ba, sun samu bayanai a takarduna na tafiya, da ke nuna cewa ni na shigo da su. Sai na rantse masu da Allah, cewa wannan kaya da su ke cewa sun gani ba nawa bane, Kuma ban san komai akan su ba. 

Bayan sun Kammala tambayata, Sai wannnan Mai tafinta ya fice daga wurin, Sai Balaraben ya fitar da takardu, ya umurce ni da in sa hannu akan su, daga nan Bayan kwana biyu, Sai suka kaini Gidan yari. Bayan wata biyu suka sake kirana, Sai suka sake yi mani tambayoyi, Ba tare da Mai tafinta ba, Sai suka yi mani larabcin makaranta, suka ce man ba ka da Kaya iri kaza da kaza? Sai na ce ma su Wallahi ba nawa ba ne. Sai suka ce toh ya akai mu ka samu sunan ka da passport number ka a kan kayan? Sai na ce masu a ina ku ka samu kayan? Su ka ce a filin jirgin Sama na Jiddah.

 Sai na ce a ina kuka kamani? su ka ce a madina. Sai na ce toh wannnan ya nuna cewa, ba kaya na  bane. Sai su ka ce za su je filin jirgi su du ba, a camera in sun samu hotona tare da jakar, ko tenfereta na hannuna akan jakar, hukunci na kisa, na ce Ma su na yarda? Na ce su du ba, daga  nan Sai suka mayar Da ni Gidan yari.

 Sai bayan shekara daya da wata biyu sai a ka ce a na kirana kotu. Da na je kotu prosikito ta karanto mun, abun da ake tuhumata da shi, na sake jaddada cewa ba jakata ba ce ban San komai akan ta ba. Daga nan sai aka dawo da ni, gidan yari. Bayan wata biyu sai kotu ta sake kirana, kuma ta wanke ni daga wannan zargin tare da ba ni takardun shaidar wanke ni. 

Daga nan sai aka sake mayar da ni gidan yari, sai aka ce an daga kara. Bayan wata uku sai kotu ta sake kira na ta wanke ni karo na biyu, aka kuma sake mayar da ni gidan yari. Bayan wasu wata uku ko hudu, aka sake kira na kotu, kuma kotu ta sake wanke ni karo na uku, tare da ba da beli ña ga ofishin jakadancin Nijeriya dake Jiddah. Aranar 24-01-2019) A jumlace, na zauna gidan yari shekara biyu. Kuma a nan waje ma yanzu watana shida, ba a sake, kira na kotu ba, kuma ba a ba ni damar komowa gida Nijeriya ba.

Da wannan ne nake kara kira ga mahukuntan kasar mu ta Nijeriya, da su taimaka su yi abun da ya kamata domin samun mafita, tare da samun damar komowa ga iyalina yau shekara biyu da rabi kenan ban sa ýaýana da iyalina a ido ba. Kuma ina kara amfani da wannan dama, ina mika godiya ta musamman ga sabon Gwamnan Jihar Zamfara Hon. Dr. Bello Matawallen Maradun, a bisa kokari da ya ke na ganin cewa an samu mafita. Da kuma su kan su ofishin jakadancin Nijeriya karkashin jagorancin Alhaji Garba Satomi Girema duk Allah ya saka musu da alkairi, ya kuma bamu mafita. Amin.

Alaramma Ibrahim Ibrahim daga ofishin jakadancin Nijeriya dake Saudiyya.
Ta hanyar Rariya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment