Thursday, 28 November 2019

Gwamnatin Sokoto ta yi wa ma'aikatan boge 8,000 afuwa

Gwamnatin jihar Sokoto ta yi wa ma'aikatan boge 8,000 da masu karbar albashin da bai dace ba afuwa.


Kwamishinan kudi na jihar Alhaji Abdussamad Dasuki ne ya bayyana hakan a wani taron manema.

Ya ce an yi hakan ne don ma'aikatan gwamnatin da suke karbar albashin da ba halalinsu ba ko suke abubuwn da ba su dace ba da su samu kwarin gwiwar bayyana kansu ga gwamnati ba tare da al'umma sun sani ba don samun afuwar gwamnati.

Za a rufe karbar afuwar ne a ranar 9 ga watan Disambar 2019.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment