Tuesday, 5 November 2019

Hukumar kwastam ta ce babu ranar bude iyakokin Najeriya

Hukumar hana fasa kwabri a Najeriya ta ce har yanzu gwamnati ba ta kayyade lokacin bude iyakokin kasar da aka rufe ba tun 21 ga watan Agusta.


Mai Magana da yawun hukumar, Joseph Attah ya shaida wa BBC cewa ba za a bude iyakokin kasar ba har sai gwamnati ta cimma burinta na rufe su.

Gwamnatin kasar dai ta dauki matakin rufe iyakokinta da Nijar da Benin a wani yunkuri na hana shigo da shinkafar waje da sauran kayayyakin da ake iya samarwa a kasar ta barauniyar hanya.

Matakin rufe iyakokin ya janyo ce-ce-ku ce a kasar inda wasu ke ganin matakin ya jefa da dama daga al'ummar kasar cikin kunci da tashin kayan masarufi.Wasu 'yan kasar na tunanin zuwa watan Janairu gwamnati za ta bude kan iyakokin bisa umurnin farko na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Amma Mista Attah ya ce kwanan watan 31 ga watan Janairun 2020 da yake jikin wata takarda da hukumar ta fitar ba yana nufin a ranar ce za a bude boda ba, saboda akwai matakai da ake bi na ganin gwamnati ta cimma manufar rufe iyakokin.

Ya ce daya daga cikin kasashe makwabtan Najeriya sun ki bin dokar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, ECOWAS da ta ce "idan kaya za su biyo ta kasar zuwa makwabtan kasashe, dole kasar ta yi wa kayan rakiya har zuwa boda."

Sai dai kuma al'ummar kasar musamman 'yan kasuwa na ci gaba da kokawa kan rufe iyakokin da suka ce ya durkusar da harkokinsu na kasuwanci.

Iyakokin kasar wadanda a baya suke cike da hada-hada, yanzu sun tsaya cik. Baya ga kayayyaki da ke rubewa da dogon layin manyan motoci a shingayen bincike da ke jiran a sake bude iyakokin kasar.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment