Monday, 11 November 2019

JAMI'AN DSS SUN HANNUNTA WASU YARA GUDA BIYU DA WASU INYAMURAI SUKA SACE A GARIN ZURU

Jami'an tsaron farin kaya DSS sun hannuta wasu yara guda biyu wadanda masu satar mutane suka sace a garin Zuru dake jihar Kebbi.


An hannunta yaran ne ga Gwamnan jahar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu. Inda ya hannuta yaran ga iyayen su.

Masu laifin mata guda biyu  da sun fito daga jahar Anambra daya daga jihar Delta, sai kuma namiji daya da ya fito daga Zuru.


 Gwamnan jahar ya jinjinawa hukumar tsaro na farin kaya  wato DSS akan namijin kokarin da suke nunawa wurin samadda tsaro a jahar Gwamnan Ya kuma kara kira Ga Al.umma da su kula da yaransu Akoda yaushe da kuma saka ido Ga sabbin fuskoki a unguwansu. Inda hukumar ta DSS ta gabatadda masu laifin a Gaban Gwamna jihar ta Kebbi.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment