Monday, 11 November 2019

Jami'an Tsaro A Filin Jirgin Sama Na Malam Aminu Kano Sun Yi Nasarar Chafke Wasu Mata Da Suka Sato Wata Yarinya Daga Kaduna Da Niyyar Safarar Ta Zuwa Legas

DA DUMIDUMINSA

Bayan da jami'an tsaron suka nemi jin bahasin me ya samu yarinyar da tunda suka zo take bacci, matan sun bayyana cewa sun sato yarinyar ne daga Kaduna kuma an ba ta maganin bacci ne da niyyar kai ta Legas.Duk wannan dai na faruwa ne lokacin da ake cigaba da musayar yawun baki akan satar yara daga Kano zuwa Anambra, ko a safiyar nan ana ta cece kuce akan bayanan da Sarkin Kano ya yi na cewa ya kamata a hukunta Iyayen da suka bari aka sace yaran su saboda sakaci.

Gaskiya lamarin satar yara a Arewa yana cigaba da daukar sabon salo, ya kamata hukumomi su dauki matakan da ya dace wajen hukunta duk wanda aka kama da irin wannan aikin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment