Thursday, 7 November 2019

Jami'an 'Yan Sanda Da 'Yan Banga Sun Budewa Masu Kasa Kayan Sana'a A Bakin Titin Mararraba/Nyaya Wuta

Rahotanni daga garin Mararraban Nyaya sun tabbatar da cewa jami'an 'yan sanda da na 'yan banga sun bude wuta kan masu kasa kaya a bakin babban titi, inda har ta kai ga an raunata mutane da dama.


Bincike ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne a yayin da wasu daga cikin masu sana'a a bakin titin suka fusata kan cin zarafin da ake yi musu a kullum, inda ake wulakanta musu kayan sana'a, inda a wasu lokutan ma konawa ake yi.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa daga cikin wadanda raunin bindiga ya raunata har da wadanda ba su ji ba su gani ba, kawai sun zo wucewa ne. 

Sannan kuma duk babu rahoton rasa rayuka, amma akwai wanda aka harba a ciki, wanda ake ganin da wuya ya rayu.

Kusan a 'yan kwanakin kullum jami'an tsaro da suka hada da sojoji, 'yan sanda, 'yan banga da sauran su sukan fito bakin titin domin tasar masu sayar da kaya a bakin hanya, inda a wasu lokutan har kona kaya suke yi.

A yayin jin ta bakin wani da lamarin ya auku a gabansa, ya ja hankalin gwamnati da cewa a wannan mawuyacin hali da ake ciki na rashin kudi da aikin yi, bai kamata tsanantawa talakan da yake fita nema domin rufawa kansa asiri ba. Tun da ba a ba shi aikin yi ba, to bai kamata a hana shi wanda yake yi ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment