Saturday, 2 November 2019

Jami'in SIB Ya Rasu A Yayin Da Yake Kan Sallar Nafila

KYAKKYAWAN KARSHE

Malam Musa Alhasan mai rike da mukamin ASP a hukumar tsaro ta farin kaya kuma daya daga cikin masu kula da tsaro a fadar gwamnatin jihar Kebbi, wanda ya rasu a yayin da yake nafila kafin sallar Juma'a a jiya a masallacin Juma'a na Dr Bello dake Birnin Kebbi, ya samu kyakykyawan zato kamar haka;


(1)Ya rasu bayan yayi raka'a ta farko ta sallar nafila kamin a tada Sallar Juma'a. 
(2) Ya rasu yana da Alwala
(3) Ya rasu ranar Juma'a. 
(4) Ya rasu ya samu kyakykawar shaida ga mutane cewa yana da rikon  addini da yawan nafiloli a koda yaushe. 
(5) Ya rasu ya samu shaidar duk wanda yake hulda da shi cewa mutumin kirki ne. 

Daga karshe an gabatar da jana'izar sa a garin Lailaba cikin karamar hukumar Argungu.

Allah ya gafarta masa kura kuransa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment