Thursday, 7 November 2019

Jihar Katsina ce ta fi mata da suka fi yawan haihuwa a Najeriya

Wani bincike da hukumar kula da yawan 'yan Najeriya, NPC da ma'aikatar Lafiya ta kasa suka gudanar ya bayyana cewa jihar Legas dake kundancin Najeriyace ke da mata wanda basu cika haihuwa da yawa a Najeriya ba inda binciken ya bayyana cewa akalla kowace mace na da 'ya'ya 3.4Ita kuwa jihar Katsina itace jiha ta Daya a Najeriya dake mata da suka fi yawan haihuwa inda binciken ya nuna cewa kowace mace ta taba haihuwa akalla sau 7.3.

An gudanar da bincikenne a shekarar 2018 data gabata wanda ya bayar da sakamakon cewa akalla matan Najeriya na haihuwa sau 5.3

Jiha ta biyu da matanta basu cika Haihuwa a Najeriya ba itace Akwa Ibom inda kowace mace haihuwa akalla sai 3.6 sai kuma Cross River da kowace mata ke haihuwa akalla sau 3.7

Jiha ta biyu kuma da matanta suka fi yawan haihuwa itace Bauchi wadda a kalla kowace mace na haihuwa sai 7.2 sai kuma Jigawa a matsayin ta 3 da kowace mace ke haihuwa akalla sau 7.1

Jihar Adamawa na da 6.1 sai Borno me 5.2 sai kuma Yobe me 5.9.

Rahoton yace matan da ke da ilimi basu cika gaihuwa ba inda matan dake da karancin ilimi sune suka fi haihuwa akai-akai hakanan kuma ya kara da cewa matan dake gidan wadata suma basi cika haihuwa ba sannan matan dake gidan talakawa sun fi yawan haihuwa.

Rahoton yace matan dake kauyuka sun fi na birni yawan haihuwa.

Sannan jihar Bauchi ce ta daya wajan yawan matan da basu kai shekaru 20 ba da suka haihu ita kuwa jihar Legas ce ke da mafi karancin irin wadannan mata a Najeriya.

An gudanar da rahotonne bisa hadin gwiwar gidauniyar Bill and Melinda Gates data da hukumar lafiya ta Duniya, WHO da majalisar dinkin Duniya da kungiyar ci gaba ta kasar kasa da kasa ta Amurka.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment