Thursday, 7 November 2019

Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila Ya Sayawa Iyayen Jaririya Dake Sansanin Gudun Hijira Gida A Katsina

Idan za ku iya tunawa cewar a ranar Litinin 16 ga watan Satumbar 2019 ne mai girma kakakin majalisar wakilan Najeriya Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ziyarci jihar Katsina, kamar yadda Hamza Ibrahim Baba mataimaki na musamman ga shugaban majalissar wakilai Hon. Femi Gbajabiamila a bangaran tallafa 'yan gudun hijira, ya ce a wannan rana suka ziyarci daya daga cikin sansanonin ƴan gudun hijirar da ke cikin garin Katsina 


Kuma a wannan lokacin ne Rt. Hon. ya haɗu wata jaririya mai suna Halima wadda aka haifa da larurar tsagaggen Lebe wanda suke tare da mahaifanta da mahaifiyar ta Nafisa da mahaifinta Abubakar wanda rikici ya rabo su daga ƙauyen Wagini dake ƙaramar hukumar Batsari, inda kakakin majalisar ya ɗaukin nauyin yiwa jaririyar aikin tiyata kuma aka samu nasarar bayan an yi har sai da ya ziyarci Asibitin ƙwararru na Royal Specialist Hospital dake Abuja domin duba lafiyar Halima.


Tun a wancan lokacin ya umarci Hamza da cewar ya bincikowa iyayen ta gida a cikin garin Katsina domin a kama musu haya har na tsawon shekaru biyu su zauna kyauta zuwa lokacin, wanda yanzu haka aka sama musu wani gida mai ɗakuna biyu aka basu a wani yanki mai kyau da tsari ga tsaro a cikin Katsina, Kakakin majalisar ya kuma ba su isassun kayan abinci da suttura kuma ana shirye-shiryen horar da iyayen yariyar domin basu abun da zasu dogara da kansu don yin kyakkyawar rayuwa. 


Kuma wannan abu ya farune bisa ga irin kiran da shugabannin Wagini dake Batsari suka yi irin su Sarkin Ruman Alh Muazu Tukur da Alh.  Dikko Muazu, kuma ya yin wannan ziyarar akwai jami’an hukumar bayar da Agajin gaggawa ta jiihar Katsina (SEMA) da jami’an ƙaramar Batsari ƙarƙashin jagorancin mataimakiyar shugabar Mata wato Hajiya Umma.

Wanda wannan ƙoƙari ne da Hon. ya yi kuma abun a yaba masa bisa wannan aikin alkairi da ya aiwatar tare da samar da ɗorewar hanyoyin magance matsalolin ƴan gudun hijirar a ƙasar nan, Kuma a ƙarshe iyayen yariyar da sauran ƴan uwa da abokan arziki sun yi murna tare da nuna farincikin su ga wannan abun arziki, inda suka yi godiya mara misaltuwa da addu'ar nasara da ci gaba ga Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment