Sunday, 3 November 2019

Kalli dan kasar China da aka haifa da yatsu 9

Wannan kafar wani dan kasar Chinane me suna Ajun da aka haifeshi da yatsu 9 a kafarshi ta hagu,shekarunshi 21 da haihuwa wannan yasa abin ya baiwa har likitocin da suka mai aiki mamaki saboda a bisa al'ada akan cire irin wannan abune tun kamin mutum ya fara girma.Ajun ya bayyana cewa wannan yatsu nashi sun saka yana rika jin kunya a makaranta kuma baida budurwa, be ma taba yunkurin yi ba dan baya tunanin akwai wadda zata so shi a haka.

Yace mahaifanshi su  ki yadda a cire mai yatsunne saboda an gaya musu cewa baiwace daga Allah.

Yace amma shi dama ya saka a ranshi cewa muddin ya girma to ba zai je a mai aiki a cire yatsun.

Ajun baida babban dan yatsa.

Likitocin da suka mai aiki sun bayyana cewa sun yi amfani da yatsar da ta yi kama da babban dan yatsane cikin sauran yatsun suka gyaramai ita ta jeru da sauran.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment