Wednesday, 20 November 2019

Kalli hotunan Huhun Rikakken Mashayin taba dan kasar China masu tada hankali

Wadannan hotunan huhun wani mutum dan kasar Chinane da ya mutu wanda rikakken mashayin taba sigarine. Mutumin dan shekaru 52 kamin ya mutu, ya saka hannu a wata yarjejeniya daya amince bayan mutuwarshi a bayar da sassan jikinshi kyauta ga marasa lafiya masu bukatar dashe.
Saidai bayan mutuwarshi aka bude cikinshi aka ga yanda Huhunshi ya lalace, ya koma baki, kamar yanda ake gani a wadannan hotuna, likitocin sun bayyana cewa ba zai yiyu a yi amfani da huhun nashi ba saboda ya lalace.


Mutumin ya shafe shekaru 30 yana shan taba sigari, dan haka huhun ya kumbura kuma yayi baki.

Lamarin ya farune a Wuxi People's Hospital dake Jiangsu inda kuma likitocin suka yanke shawarar saka lamarin a shafin Youtube dan Duniya ta gani ko hakan zai zama Izina ga masu shan taba da kuma wanda ke da sha'awar fara sha.

Kuma an kalli bidiyon sama da Sau Miliyan 25.

Mutane Miliyan 1.2 ne ke mutuwa duk shekara sanadin shan taba Sigari wadda kuma tana taimakawa wajan samar da Cutar Dajin Huhu me saurin kisa.

Kalli bidiyon lamarin a kasa:
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment