Friday, 15 November 2019

Kalli yanda Cristiano Ronaldo ya sacewa wani waya

Wani lamari ya faru tsakanin tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo da wani masoyinshi da ya dauki hankulan mutane sosai musamman a shafukan sada zumunta.Abinda ya faru shine Ronaldo ya koma kasarshi Portugal inda yake buga mata wasannin samun shiga gasar Euro 2020.

Yana cikin tafiya a kan titi sai ya hango wani masoyinshi dake daukar shi hoto da waya.

Sai ya lallaba ya kwace wayar daga hannunshi cikin Raha.

Daga baya Ronaldon ya mayar mai da wayarshi inda shi kuma ya cika da farin ciki.

Kalli bidiyon yanda lamarin ya faru a kasa:


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment