Monday, 11 November 2019

Kalli yanda Kocin Man City ya haukace bayan da Liverpool ta ci su 3-1

Bayan wasa me daukar hankula da aka buga a jiya tsakanin Liverpool da Me rike da kofin Premier League, Man City wanda Liverpool din ta ci 3-2, abubuwa da yawa sun faru da suka fauki hankula a wasan musamman akan me horas da 'yan wasan na Man City, Pep Guardiola.Sadio Mane da shine ya ci wa Liverpool kayatacciyar kwallo ta 3 da ya sakawa kai ta shiga raga, an ganshi yana gaisawa da kocin Man City, Guardiola yana murmushi. A baya dai Guardiola ya taba magana akan Mane inda yace ya cika kwanciya da gangan a gidan abokan wasa dan neman a bashi bugun daga kai sai gola.

Bayan kammala wasan da Kwallon Mohamed Salah wadda wasu ke ganin yayi satar gida amma Na'urar VAR ta tabbatar da ita sannan kuma da kwallon hannun da dan wasan Liverpool Alexander-Anold yayi a gidan Liverpool din wadda shima ba'a baiwa Man City bugun daga kai sai gola ba, kocin Man City, Guardiola har ila yau ya sake zuwa wajan alkalan wasa inda ya gaisa dasu yana ce musu na gode( da ba'a).

Hakanan an kuma ga Guardiola yana wani abu kamar hauka-hauka yana daga yatsu biyu sama, watau alamar sau 2 ana cutarsun, wannan abu ma ya dauki hankula sosai, kalli lamarin a kasa:


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment