Sunday, 17 November 2019

Kalli yanda Ronaldo ya rufewa 'yan kasar Luxembourg masu mai Ihun Messi! Messi baki

Tauraron dan kwallon kafar Portugal, Cristiano Ronaldo ya kai kasarshi ga gasar Euro 2020 a yau bayan da ya ci kwallo ta biyu a wasan da Portugal din talallasa Luxembourg 2-0Fernandez ne ya fara ciwa Portugal kwallo ta farko ana mintuna 39 kamin tafiya hutun rabin lokaci.

Magoya bayan Luxembourg sun rika wa Ronaldo ihun Messi! Messi!! Saidai ana gaf da tashi wajan mintuna 86 sai ga Ronaldo ya saka kwallo ta biyu inda ya rufewa masu mai ihun baki. Yayin da yake murnar cin kwallon, Ronaldo ya daga kai sama alamar jin masu mai Ihu ina suke?


Wannan kwallo da yaci itace ta 99 da ya ciwa kasarshi.

Akan na nufin ya fi Messi ciwa kasar kwallaye da guda 30
Yafi Pele viwa kasarshi kwallaye da guda 22
Yafi Maradona ciwa kasar kwallaye da guda 65
Yafi Neymar ciwa kasarshi kwallaye da guda 38
Ya kuma fi Ronaldo Nazario na Brazil ciwa kasarshi kwallaye da guda 37.

Har yanzu dai Tsohon dan kwallon kasar Iran Ali Daei ne kawai ya fi Ronaldo ciwa kasar kwallaye inda yake da guda 109.

Saidai wasu sun yiwa Ronaldon ba'a akan kwallon da yaci ta yau inda sukace dama tana kan layine zata shiga raga ya karasata kamar yanda za'a iya gani a hotonnan na kasa:

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment