Friday, 15 November 2019

Kalli yanda Ya mutu sanadiyyar jan wuta yayin da yake kallon kwallo a wayarsa

Wani masoyin kwallon kafa a kasar Thailand, Somchai Singkhorn dan shekaru 40 kenan da ya mutu a sanadin Jan wutar Lantarki.'Yan sanda sun bayyana cewa an sameshi da wayarshi anjone da Chaji sannan abin sauraren magana a makale a kunneshi, sun ce da farko an yi tsammanin ko wutace ta jashi ya mutu.


Amma kuma an iske kwalbar giya a dakin nashi dan haka za'a yi bincike dan kamin tabbatar da sanadin mutuwar tashi.

Rahotannin farko dai sun ce mutumin ya mutune yayin da yake kallon kwallo a wayarshi kuma wuta ta jashi.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment