Monday, 4 November 2019

Kotun daukaka kara ta tsige Ado Doguwa

Kotun Daukaka Kara da ke zama a Kaduna ta tsige shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya, Ado Doguwa daga kujerar dan majalisa.


Jaridar Daily Nigerian ne ta ruwaito wannan labari inda ta tabbatar da haka a shafinta.

Honarabul Doguwa na wakiltar kananan hukumomin Tudunwada da Doguwa ne a majalisar Tarayya.

Idan ba a manta ba Kotun ta tsige dan majalisan tarayya dake wakiltan Bebeji/Kiru, Jihar Kano Abdulmumini Jibrin.

Alkalin Kotun Adejoje Adepoju wadda shine ya yanke wannan hukunci ya bayyana cewa dalilin da yasa kotu ta tsige dan majalisar shine ganowa da akayi cewa takardun da aka shigar da sakamakon zaben wa wancan lokaci ba sune ya kamata ayi amfani da su ba. Sannan kuma duk an lalata na ainihin.

Maishari’a Adepoju ya ce a dalilin haka dole ya sole zaben kwata-kwata.

Ya umarci hukumar zabe da ta sake gudanar da zaben dan majalisar tarayya na wannan kananan hukumomi biyu.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment