Sunday, 3 November 2019

Kuskuren turanci a lambar motar "Majalisar Kano" ya jawo cece-kuce sosai

Wannan hoton na sama lambar motar bulalar majalisar jihar Kanone wanda ta watsu sosai a shafukan sada zumunta saboda kuskuren da aka yi wajan rubutun da turanci a jikin lambar an rubuta "Chip Whip" wanda kuma ainahin yanda rubutun yake "Chief Whip" ne.Cece-kucen da wannan lamari ya jawo a shafukan sada zumunta yayi kamari sosai ta yanda har sai da hukumar dake kula da hadurra ta FRSC ta fito ta nesanta lanta da wannan lambar mota.

Ta bayyana cewa ba ita ce ta yi wannan lamba ba kuma tasa jami'inta dake Kano yayi bincike akan wanda yayi wannam lamba dan hukunta shi.

Saidai a Nashi martanin,Bulalar majalisar Kano, Honorable Ayuba Durum ya bayyana cewa shi bashi da ma motar aiki da aka bashi tukuna kuma hotunan wata lamba da aka dangantashi da ita dake yawo a shafukan sada zumunta wasu batagari ne kawai suke yi dan batawa jama'ar Kano suna, kamar yanda ya shaidawa Daily Trust.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment