Wednesday, 6 November 2019

Kwana daya bayan mai aikin Mummunan raunin da ya ji, An sallami dan wasan Everton, Gomez daga Asibiti

Kwana daya kacal bayan mummunan raunin da tauraron dan kwallon kasar Portuga me bugawa Everton wasa dan shekaru 26 ya ji a wasan da suka buga da Tottenham da ya kare da sakamakon 1-1, An sallameshi daga asibiti.
Gomez ya ji rauninne dai yayin karon battar da suka yi da Son inda ya samu gocewar kashi data dauki hankulan Duniyar kwallo.

Saidai Ranar Litinin din data gabata, an wa Gomez aiki a asibiti kuma Ranar Talata kungiyar ta Everton ta bayyana cewa an sallami dan kwallon daga Asibiti inda yanzu tawagar likitocin kungiyar zasu ci gaba da kula dashi.

Ana dai tsammanin Gomes zai kwashe watanni 6 zuwa shekara 1 kamin ya koma fili ya ci gaba da buga kwallo.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment