Saturday, 2 November 2019

Kwarankwatsa ta fado tare da kashe mutane 10 a Indiya

Mutane 10 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar kwarankwatsa a jihar Maharashtra dake yammacin Indiya.


Labaran da jaridun Indiya suka fitar sun ce a yankunan Akola, Amravati da Nanded dake jihar Maharashtra ne kwarankwatsar ta fado tare da kashe mutane 10.

Mahukuntan sun ce mamakon ruwan sama ya mamaye dukkan jihar.

Akalla a kowacce shekara mutane dubu 2 kwarankwatsa ta ke kashe wa a Indiya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment