Thursday, 7 November 2019

Lalacewar titunan Najeriya ba ta kai yanda ake ta yayatawa ba>>Ministan Ayyuka, Fashola

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ya bayyaba cewa irin yanda ake yayata lalacewar titunan Najeriya lamarin bai kai haka ba. Ya bayyana hakane a jiya, Laraba bayan kallama taron majalisar zartaswa.
Fashola yace titunan Najeriya basu yi lalacewar da ake yayata cewa sun yi ba, yace nasan wannan magana da na yi zata zama kanun labarai amma maganar gaskiya itace titunan basu kai lalacewar da ake yayatawa ba.

Fashola ya kara da cewa idan akace an amince ayi amfani da kudi wajan yin aiki bawai hakan na nufin an bayar da kudin bane, yace Ma'aikatar kudi da sauran wasu ma'aikatu na yayata matsalar kudin da ake da ita yayin da suke bayar da kudin ayyuka kuma Najeriya ta kwashe shekaru da dama tana fana da gibi a tattalin Arzikinta.

Sannan idan akace za'a fara aiki akwai abubuwan da ya kamata a fara lura dasu, ba daga yin maganar aikin zai fara ba, akwai matakai da ya kamata abi, kamar kai ijinan aiki wurin da za'a yi aikin, da sayen rodi da sauran wasu kayan aiki wanda kamfanonin da ake baiwa kwagila bawai suna dasu a ajiye bane, sai an siyo.

Ya kara da cewa, kamar maganar fasa dutse sai an nemi amincewar ma'aikatar tsaro ta bada damar sayen nakiyoyin da za'ayi amfani dasu da kuma ma'aikatar shari'a dadai sauran wasu matakai da ake bi kamin fara aiki.

Fashola ya kara da cewa, suna jira damuna ta wucene dan fara ayyuka gadan-gadan.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment