Tuesday, 5 November 2019

Lewandowski ya shiga gaban Messi wajan yawan kwallaye a bana

Tauraron dan kwallon kasar Poland me bugawa kungiyar Bayer Munich wasa, Robert Lewandowski ya shiga gaban Messi a shekarar nan ta 2019 a yawan cin kwallaye kuma idan Messin be yi da gaske ba zai rasa takalmin zinare da ake baiwa wanda yafi yawan cin kwallaye a shekara a turai da a yansu Messin ne ke rike dashi.
Lewandowski dai na da kwallaye 38 a wasanni 38 da ya buga a shekarar. Wannan na nufin yana gaba da Mesii da yawan kwallaye 2 inda shi Messin yanzu yake da yawan kwallaye 36 a wasa 39 da ya buga a bana.

Na ukun su shine matashin dan kwallonnan na kasar Faransa, dan shekaru 20 me bugawa kungiyar PSG wasa, inda yake da yawan kwallaye 31 a wasanni 32 da ya buga a bana.

Saura dai kasa da watanni 2 shekarar ta kare, masu iya magana na cewa ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment