Monday, 11 November 2019

Liverpool ce kungiya ta daya a Duniya inji kocin Man City bayan da Liverpool din ta musu ci 3-1

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa Man City dake rike da kofin Premier League, 3-1 a wasan da suka buga na yau na gasar cin kofin Premier League na bana.

Fabinho, Mohamed Salah da Sadio Mane ne suka ciwa Liverpool kwallayenta sai kuma Bernardo Silva da ya ciwa Man City kwallonta.

An yi korafi akan hukuncin na'urar VAR a wasan na yau, inds a farkon wasan kamin Liverpool ta ci kwallon farko dan wasanta na baya, Trent Alexander-Anold ya taba kwallo da hannunshi a gidan na liverpool bisa Kuskure wanda kuma alkalin wasa be baiwa City bugun daga kai sai me tsaron gida ba hakanan VAR ta tabbatar da wannan hukinci nashi.

Sannan kwallon MoSalah ana mata kallon a matsayin satar gida amma itama Na'urar ta VAR ta tabbatar da ita.

Wasan na yau ya dauki hankula sosai inda da wannan nasara a yanzu Liverpool ta baiwa City tazatar maki 9 kenan.

Da wuya Liverpool ta yi rashin nasara a wasanni 3 nan gaba dan kuwa tun daga kakar wasan bara har zuwa yanzu wasa daya tal Liverpool ta yi rashin nasara akanshi, wanda suka buga da City din a farkon shekarar nan.

Bayan kammala wasan, Kocin Man City, Pep Guardiola ya bayyana cewa ba abune me sauki yin wasa tare da kungiyar da itace ta daya a Duniya ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment