Thursday, 28 November 2019

Liverpool ta sha da 1-1 a hannun Napoli: Haaland ya kafa tarihin da babu irinshi

Wasa ya so ya jikewa Liverpool a karawar da suka yi da Napoli a daren yau a gasar cin kofin Champions League, Napoli ce ta fara cin Kwallo inda daga baya Liverpool ta rama ta hannun Loveren kuma a haka aka tashi wasan da sakamakon 1-1.Liverpool a yau bata taka wata rawar a zo a gani ba amma kwallon da Loveren ya ci da kai ta kayatar.

Kalli kwallon ta Lovren


Wasa na gaba a rukunin E shine tsakanin Genk da Red Bull wanda Red Bull ta hukunta Genk da ci 4-1, tauraron dan matashin dan wasan Red Bull, me shekaru 19, Haarland a yauma ya ci kwallo.Wannan tasa ya kafa tarhin zama matashin dan kwallo na farko dan kasa da shekaru 20 da ya jera wasannin gasar Champions League 5 yana cin kwallo a kowanne.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment