Saturday, 2 November 2019

Lukaku ya ciwa Inter duka kwallaye 2 data ci Bologna a yau

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta lallasa Bologna da ci 2- a wasan da suka buga yau na gasar cin kofin Serie A. Lukakune ya ciwa Inter duka kwallayen nata.Kwallayen da Lukaku ya ci yau sune na 9 daya ciwa Inter a wasanni 11 daya buga, dan wasan daya taba yin irin wannan bajinta shine Ronaldo Nazario dan kasar Brazil a shwkarar 1997/98.

Lukaku dai zai yi farin ciki da barin Man Unted da yayi zuwa Inter tunda ga tauraruwarshi sai haskakawa take.

Itama dai Juventus ta yiwa Torino ci 1 me ban haushi ta hannun dan wasan bayanta data siyo daga Ajax, De Ligt wadda itace kwallonshi ta farko a kungiyar.

A farkon fara wasan na yau De Ligt ya taba kwallo da hannu a gidansu saidai ba'a baiwa Torino bugun daga kai sai gola ba.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment