Friday, 8 November 2019

'Mai shan shisha' ta kusa tayar da wuta a jirgin Azman

Yaya za ku ji idan kuna cikin jirgi a sararin samaniya sai kuka ga hayaki yana tashi daga wani bangare na jirgin?


Wannan shi ne tashin hankalin da fasinjojin jirgin Azman mai tafiya Abuja daga Legas suka samu kansu a ciki, jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin sama na Murtala Muhammad ranar Alhamis.

Lamarin ya tilasta wa jirgin komawa Legas don yin saukar gaggawa domin gudun afkuwar wani bala'i.

Sai dai da saukar jirgin sai aka gano ashe wata matashiya ce ta buya a cikin bandakin jirgin tana 'busa tabar shisha'.
Wani jami'in kamfanin Azman— wanda ba ya son a ambaci sunansa —ya tabbatar wa BBC cewa "tuni jami'an tsaro suka tafi da matar."

Bayan hakan ne kuma aka shafe tsawon sa'a hudu ana binciken jirgin don gano ko yana da wata matsala daban bayan hakan, amma sai hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen saman Najeriya suka tabbatar da lafiyarsa.

Daga bisani jirgin ya tashi zuwa Abuja kamar yadda aka tsara.

Wata fasinja da ke cikin jirgin ta shaida wa BBC cewa al'amarin ya faru ne lokacin da aka lura hayaki na fito wa daga cikin jakar matar, inda nan da nan kuma sai ta shige ban daki.

Daga nan ne sai kararrawar jirgi mai nuna alamar akwai matsala ta fara kadawa, abin da ya ja hankalin ma'aikatan jirgin suka bude ban daki aka kuma ga matar.

Ta ya ya za a wuce da shisha jirgi duk da tsaro?
Wannan ce tambayar da za ta zo wa mutane da dama a rai.

Sai dai a lokacin da sashen BBC Yoruba ya tuntubi hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya FAAN kan wannan tambaya, sai wani jami'inta ya ce "abu ne da ba zai yiwu ba a wuce duk shingayen binciken da ke filin jirgin ba tare da an gano ba."

Kamfanin Azman ya ce nan ba da jimawa ba zai fitar da sanarwa mai dauke da cikakken bayani kan batun.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment