Saturday, 2 November 2019

Masarautar Daura Ta Naɗa Musa Haro A Matsayin Ɗan Madamin Daura

A yau Asabar ne 2 ga watan Nuwanba 2019 masarautar Daura aka yi gagarumin taron bikin naɗi wanda mai martaba Sarkin Daura Alhaji Dakta Umar Farouk Umar ya naɗa Alhaji Musa Haro a matsayin Ɗan Madamin Daura wanda ɗane ga yayar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kuma an yi kasaitaccen biki da aka jima ba a yi kamar sa ba a masarautar.


Taron bikin naɗin ya samu halattar mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo GCON, shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, mataimakin gwamnan jihar Katsina Alh. Mannir Yakubu, gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, gwaman jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Rt. Hon Alhassan Ado Doguwa, mataimakin gwamnan jihar Sokoto tare da Sanatan shiyar Daura Ahmad Babba Kaita da sauran manyan jami'an gwamnatin tarayya dana jihar Katsina da maƙoftan ta a cikin da wajan Najeriya duk hallara a garin Daura, kuma an yi taro lafiya an kammala lafiya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment