Friday, 8 November 2019

Masari Ya Gargadi Jami'an Hukumar Kwastam Da Su Daina Harbe-harbe A Cikin Garin Katsina

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya gargadi jami’an Hukumar Hana Fasa Kwabri ta Kasa saboda yadda suke haddasa asarar rayukan jama’a a lokacin gudanar da aikinsu a jihar Katsina.


Gwamna Masari wanda ya ce ya kamata jami’an su lalubu wata hanyar ta daban wanda za su mutunta dangantakar da ke tsakaninsu da al’ummomin da ke zaune kusa da kan iyakoki da kuma cikin gari domin kaucewa kisan ba gaira ba dalili.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar mai kula da ayyuka na musamman akan iyakokin Najeriya a jihar Katsina (National Border Drill Operation) Mataimakin shugaban Hukumar ACG Bashir Abubakar tare da hadin gwiwa sauran jami'an tsaro masu kula da yadda aka rufe kan iyakokin, a gidan gwamnatin Katsina.

Haka kuma Gwamnan ya Kara da cewa gwamnatinsa ta bada fifiko wajan kare rayuka da dukiyoyin al’umma ne, saboda haka ba za su lamunci kisan ba gaira ba dalili ba daga jami’an Hukumar Hana Fasa Kwabri ta Kasa ba a lokcin gudanar da aikinsu.

“Ina tunanin ya kamata su zama kamar fararan hula wajan tafiyar da aikin da doka ta baku damar yin, yin amfani da harbin bindiga acikin gari, ba za mu laminta ba, komi za ku yi, ku yi shi can cikin da ji, ko kuma akan iyakoki” inji Masari 

“Za mu cigaba da bada duk wata gudummawa da da ku ke bukata a ya yin wannan aikin naku, abinda kawai muke so daga wajanku shi ne ku daina yin harbe-harbe a cikin garin wanda hakan yana haifar da razani da tsoro ga jama’a, saboda hakan yana san jama’a su riqa gudu a ya yin da wasu ke samun munanan raunuka wasu kuma suna rasa ransu.” Inji Gwamna Masari.

Gwaman Masari wanda ya jaddada cewa idan suka shiga cikin gari yin aikinsu su kaucewa dabi’ar nuna karfin bindiga akan jama’a, abinda ake tsoro qarar bindiga kuma hakan shi zai fi saukin wajan gudunar da aikin tare da samun nasarar da ake buqata.

Kazalika Gwamna Aminu Masari ya yi kira ga tawagar da su sanya masu rike da masarautun gargarjiya da shuwagabannin addini wajan tafiyar da wannan aikin na hana fasa kwabri da sauran ayyukan a jihar Katsina da kuma kasa baki daya. 

Tunda farko da yake nasa jawabin shugaban tawagar ayyukan na musamman akan iyakokin Najeriya ACG Bashir Abubakar ya ce wannan tawaga ta su domin su samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya da kuma dawo da martabar tattalin arziki kasa ta hanyar bada kariya akan iyakokin ta qasa da masana’antu

Ya ce ya zuwa yanzu sun samu nasarra kama motoci 288 ta tare buhunan shinkafa ‘ya kasar wajen mai yawa da sauran abubuwan da aka shigowa da su, sai ya yi kira ga Gwamnan Masari ya ba su goyan bayan domin gudanar da wannan aiki na su yadda ya kamata.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment