Saturday, 2 November 2019

Mbappe ya shiga gaban 'yan kwallon Duniya bayan da ya ci kwallaye 100 a wasan da PSG ta sha kashi a hannun Dijon

Tauraron dan kwallon kasar Faransa me bugawa kungiyar PSG wasa, Kylian Mbappe ya kafa tarihin ciwa kungiyoyin da ya bugawa kwallo kwallaye 100, sai Ranar 20 ga watan Disamba me zuwa Mbappe zai cika shekaru 21 da haihuwa.
Wannan na nufin Mbappen ya kafa wannan tarihi da sauri fiye da manyan taurarin 'yan kwallon Duniya irin su Cristiano Ronaldo, Suarez, Zlatan Ibrahimovic, Messi da Rooney.

Mbappe ya ci kwallon tashi ta 100 ne a wasan da suka buga a jiya da Dijon dake karshen teburin gasar League 1 wadda ta basu mamaki inda ta yi nasara a kansu da ci 2-1.

Wannan itace rashin nasara da ta 3 kenan da PSG ta yi a kakar wasan bana sannan ta 8 a shekarar 2019, rabon ta da irin wannan rashin nasara tun shekarar 2010.

Hakanan a wasan na jiya, Mbappe ya nuna wata bajinta data kayatar da mutane sosai inda ya taro wata kwallo da ta yi shirin fita waje ya kuma sakwa dan wasan bayan Dijon Osi.

Kalli hotuna da Bidiyon yanda lamarin ya faru a kasa:
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment