Monday, 11 November 2019

Me Ya Sa Malamai Suka Yi Shiru A Yanzu Da Ake Tsadar Rayuwa A Nijeriya?

A halin da ake ciki na kunci da tsadar rayuwa, da dama daga cikin Malamai sun zabi su yi gum da bakunan su. 


Amma in lokacin za be ya zo su ne a gaba gaba wajen magana.

Domin sauke nauyin da ke kaina duk da cewa Ina da rauni, Ina so in Yi amfani da wannan kafa don ba da shawara.

Wajibi ne Malamai su wa talaka adalci wajen Kira ga shuwagabanni, a lokacin da aka Sami tsadar rayiwa, don shuwagabanni su tuna hakkin da ke kansu.

Rashin yin haka ya saba wa manhajin magabata na kwarai.

Domin kada wanda bai sani ba ya tsanmaci cewa ra'ayi na ne wannan, ga hoton daya daga cikin dunbin wasiku da manyan magabata ke rubutawa a kan haka.

Al Imam Nawawi ne ya rubuta wa Sarki Alzahir yana tunatar da shi hakkin da ke kan shi na ba talaka kulawa.

Allah Ya sa mun dace.
Sheikh Nuru Khalid.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment