Wednesday, 27 November 2019

Messi ya kafa tarihin da babu irinshi a wasan da Barcelona ta lallasa Dortmund da ci 3-1: Lukaku ya haskaka sosai a wasa me cike da dambarwa da Inter ta wa Slavia Prague 4-1

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta hukunta Borussia Dortmund da ci 3-1 a wasan da suka buga na gasar cin kofin Champions League a yau. Messi, Suarez da Griezmann ne suka ciwa Barca kwallayen.Messi, kamar ko da yaushe ya haskaka a wasan na yau inda ya bayar da taimako akan ci kwallaye 2 sannan kuma ya ci kwallo shima, wasan da yayi a yau shine na 700 da ya bugawa Barca sannan yaci jimullar kwlalaye 613 da bayar da taimako aka ci 249, ya ci kwallaye 3 a wasa daya sau 40 sannan yaci kofuna 34 da Barca.

Hakakak Messi ya kafa tarihin da shi kadai ne ke da irinshi a kwallon kafa inda ya ci kungiyoyi 34 a gasar ta Champions League.

Wasa na gaba a rukunin F shine wanda aka buga tsakanin Slavia Prague da Inter Milan, abinda aka yi a wasan ya dauki hankula sosai.

Tsohon dan wasan Man United,Lukakune ya fi daukar hankula sosai a wasan inda ya bayar da taimako me kyau aka ci kwallon farko sannan ya ci kwallo ta biyu amma na'urar VAR ta kashe ta sannan ta bayar da bugun daga kai sai gola ga Slavia Prague a wani abinda aka yi a baya, wannan hukunci ya jawo cece-kuce.

Saidai duk da haka, kamin a tashi wasan sai da Lukaku ya ci kwallaye 2, Martinez shima ya ci kwallaye 2 inda aka tashi wasan 4-1.

Lukaku Ya ci jimullar kwalaye 250 kenan a tarihinshi.

Kalli kwallayen na Lukaku a kasa:
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment