Tuesday, 5 November 2019

Ministan Sadarwa, Sheik Pantami Ya Umarci Kamfanonin Sadarwa Su Rage Farashin Sayen Data

Gwamnatin Nijeriya ta umarci hukumar sadarwa ta kasa, NCC, ta tilasta ma kamfanonin sadarwar tare da samar da wani tsari da zai tabbatar da rage farashin sayen ‘Data’ da yan Najeriya suke yi, domin kuwa yan Najeriya na kokawa a kan tsadarsa. 


Jaridar The Nation ta ruwaito ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami ne ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin shuwagabannin gudanarwar hukumar NCC a karkashin jagorancin Sanata Olabiyi Durojaiye. 

 Pantami ya bayyana ma bakin nasa cewa yan Najeriya da dama suna kai masa korafe korafe game da tsadar farashin sayen Data idan aka kwatanta da suaran kasashen nahiyar Afirka. 

“Ina kira ga shugabancin NCC dasu tabbata su rage farashin sayen Data a Najeriya saboda yan Najeriya da dama suna kokawa game da tsadar Data, idan kuka je wasu kasashen, hatta kasashen da basu kai Najeriya yawan jama’a ba ma za ka ga cewa farashin Data bai kai namu ba. 

“Ni kaina wannan matsalar ta shafeni, sai ka ga mutum yasa loda kati ya sayi Data, tun ma kafin ka yi amfani da kashi 20 na Datan kwatsam sai ga komai ya tafi.” Inji shi.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment