Friday, 8 November 2019

Muhimman Bayanai Akan Tukunyar Gas

'Gas cooking cylinder', yana da mummunan hadarin da ba zai gaza na bam ba idan ya yi 'expire', yana da amfani matuka, kuma yana taimakon talaka ko dalibai wurin girki, amma ga wata sanarwa ga dukkan masu amfani da ita sai su kula domin tseratas da rai da lafiya, kowane Cylinder yana da lokacin lalacewar sa wato Expiry date ko month ko year, kuma a jikin sa ana rubutawa.

Sau da yawa ana rubutawa da alphabets kamar A, B, C, ko D, ga abinda sune nufi:-
A is for March, 1st Qtr
B is for June, 2nd Qtr
C is for Sept, 3rd Qtr
D is for Dec, 4th Qtr.

Sannan a bayan sa ko gefe akwai wasu lambobi guda biyu da harafi daya, ga misali, D06, idan kaga D06 a jikin cylinder din ka na girki to ana nufi (Expire in December 2006, abin nufi ya lalace tun 2006, shekaru 13 da suka wuce, dan haka komai zai iya faruwa daga wannan Gas cooker din.
.
Misali na biyu, idan kaga A20, to ana nufin zai lalace ko Expire a watan uku wato March na 2020, nan da watanni 8 masu zuwa, dan haka idan kaje saya sai ka lura kada ka sayo wanda ya zamo expired, domin idan yayi expire at anytime zai ita fashewa ya kashe mutum ko ya raunata mutum ko kuma ya sabbabba gobara, sai a kula idan kaje saya ka duba Kai da kan ka, kafin ka saya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment