Saturday, 30 November 2019

Muna Kira Ga Babban Bankin Nijeriya Da Ragowar Cibiyoyin Bayar Da Rance Da Su Cire Ribah ('Intrest) Ciki Basussukan Da Suke Bayarwa, Inji Sheikh Bala Lau

Shugaban Kungiyar Izala na Tarayyar Najeriya, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira da babbar murya ga babban bankin Najeriya CBN, da kuma sauran hukumomi da cibiyoyin da suke bayar da tallafin rance ga yan kasa Najeriya.


Shi dai tsarin Interest, wato RIBAH, ya sabawa karantarwar addinin Musulunci, kuma Allah madaukaki yayi hani ga hakan, sannan Allah yayi alkawarin mummunar azaba ga wadanda suke ta'ammuli da kudaden ribah.

Wannan hanin da Allah madaukaki yayi akan kudin Ribah, ya sa dole duk musulmi na gari ya kauracewa duk wani kudin ribah, wanda ake kira a turance da 'Interest'.

Sheikh Bala Lau yace "musulmai da yawa suna kauracewa bashin da babban bankin Najeriya CBN yake bayarwa da sunan tallafin Noma, da sauran abubuwan more rayuwa, domin su kubuta daga waccan doka da ta hanasu amfani da kudin Ribah".

"Kenan in har babban bankin Najeriya, da sauran hukumomin bayar da rance zasu dinga bayar da bashi da ribah; toh kenan a fakaice kamar sun haramtawa musulmai cin moriyar tsare-tsaren nasu, tunda su musulmi addininsu ya hanesu aikata hakan. Kuma in har hakan ta tabbata, toh zai zama barazana ga tattalin arzikin musulmin kasar Najeriya". Inji Sheikh Bala Lau.

Shugaban ya kara da cewa " lallai akwai bukatar janye Interest daga tsarin basussuka da ake bayarwa, dokan kada fushin Allah ya sauka akan kasa Najeriya. Domin Allah yayi alkawarin saukar da fushinsa akan duk al'ummar dake mu'amala da ribah.

A karshe Shehin Malamin yayi kira ga majalisar dattijai da waakilai na kasa, dasuyi tsarin da zai taimaki musulmi samun rance da ba Ribah a ciki. 

Muna fata wadannan hukumomi zasu fadaka kuma su gyara wannan tsari domin bawa kowanne dan kasa cin moriyar wadannan tsare-tsaren nasu.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment