Monday, 4 November 2019

Na Tuba Allah ka yafeni>>Hadiza Gabon bayan kakkausan martanin da ta baiwa wani da ya mata kalaman da basu dace ba: Ministan Sadarwa, Pantami ya jinjina mata

Allah sarki, bayan kakkausan martanin da tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta wa wani da ya mata maganar da bata dace ba bayan ganin hotonta tare da abokan aikinta, Rahama Sadau da Fati Washa, Hadizar ta fito ta nemi gafarar Allah.A shafinta na Twitter inda nanne lamarin ya faru, Hadiza ta bayyana cewa ta goge wancan kakkausan martani data wa wancan bawan Allah sannan kuma tace ta tuba tana rokon Allah ya yafe mata saboda mayar da martani da kuskure bisa kuskuren da aka mata.

Wannan tuba da ta yi ya dauki hankula sosai inda da dama suka yaba mata ciki kuwa hadda shahararren malamin addinin Islama kuma Ministan Sadarwa, Shiekh Dr. Isa Ali Pantami inda yace wannan tuba da ta yi abin yabawane sosai kuma Allah ya gafarta mana.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment