Wednesday, 27 November 2019

Na Ya Yaba Da Rufe Boda Da Buhari Ya Yi>>Obasanjo

Tsohon Shugaban kasar Nijeriya, Janar Olusegun Obasanjo ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan matakin da gwamnatin Nijeriya ta dauka na garkame kan iyakokin Nijeriya.


Obasanjo ya yi wadannan kalamai ne a birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia yayin wani babban taron cinikayya na kasashen Afirka. 

Obasanjo ya kuma yi na'am da matakin gwamnatin Buhari tare da yin kira ga Jamhuriyar Benin da ta samo wasu ingantattun hanyoyi na cinikayya da Najeriya. 

A cewar Obasanjo, rufe iyakokin mataki ne mai matukar kyau idan aka yi la'akari da yadda wasu kasashen suka maida Nijeriya bolar zubda komatsen su. 

Obasanjo yace "Ba mu da matsala game da kayayyakin da aka kera a Jamhuriyar Benin, muna maraba da su. Amma wasu kayan da ake shigowa dasu Benin babban matsala ce ga Najeriya idan har aka bada damar hankado su zuwa Nijeriya".
Daga Haji Shehu.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment