Friday, 29 November 2019

Nan bada dadewa ba za'a fara aikin Ajiye Bututun Gas daga Kudancin kasarnan zuwa jihohin Kogi, Kaduna da Kano

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan gaba kadan za'a fara aikin ajiye bututun man iskar Gas daga kudancin Najeriya zuwa Lokoja, Kaduna da Kano.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan taron kasashen dake fitar da man gas zuwa kasashen waje da aka yi a kasar Equatorial Guinea a yau, Juma'a da ya halarta.


Shugaban ya kara da cewa ya kamata kasashen Afrika su hada kai dan amfani da iskar Gas wajan magance matsalar makamashi da ake fama da ita a Yankun Afrika.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment