Friday, 8 November 2019

Osinbajo ya musanta cewa shugaba Buhari ya kori Hadimanshi daga aiki

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya musanta labarin da jaridar Daily Trust ta buga jiya inda ta wallafa sunayen wasu hadimanshi da ta ce shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya sallama daga aiki.Me taimakawa Osinbajon ta bangaren kafafen sadarwa, Laolu Akande ne ya bayyana haka ta shafinshi na Twitter inda yace sunayen hadiman mataimakin shugaban kasar dake yawo ana cewa an koreau ba gaskiya bane.

Ya kuma kara da cewa, wani lamari da ya faru tsakanin wani dan jarida da jami'in tsaron Osinbajon an warware matsalar kuma an baiwa dan jaridar Hakuri.

Jaridar Punch ma ta bayyana hira da ta yi da wasu daga cikin hadiman Mataimakin shugaban kasar da akace an kora daga aiki inda sukace basu samu hakan a hukumance ba suma sun gani a labaraine dan haka zasu je wajan aikinsu.

Wasu kuwa daga cikinsu sunje labarin ba gaskiya bane.

Saidai binciken da jaridar ta yi ya bayyana cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai san da sallamar hadiman mataimakin shugaban kasar ba, saidai dama akwai tsarin canja musu wajan aiki.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment