Monday, 11 November 2019

Rahotonni Na Nuna Cewa Akwai Sauran Yara 49 Da Aka Sace A Kano

Ga dukkan alamu akwai sauran aiki a batun gano yaran da wasu batagari su ka sace su daga Kano su ka kai su kudu maso gabashin kasar. Hasali ma har yanzu wasu iyaye na cigaba da kokawa kan rashin gano 'ya'yansu duk da ankarar da hukumomi da su ka yi tuntuni.
Biyo bayan yadda Muryar Amurka ta gudanar da taro don zantawa a kan kalubalen sace yara, wasu iyayen yara da su ka kawo rahoton an sace 'ya'yansu, sun taru a Kano don bukatar hukumomi da sauran jama'a su taimaka wajen gano yaran.

In za a tuna bayan nasarar ceto yara 9 da 'yan sanda suka yi wadanda yawanci a ka sayar da su a Anaca jihar Anambra, wasu iyaye sun kawo rahoton cewa an sace masu yara 49.

Iyayen dai sun bukaci a tsananta bincike don kubutar da 'yaran da su ke sa ran su na raye, wadanda a baya su ka zaci ko matsafa ne su ka sace su don ayyukan tsafi.

Daya daga iyayen al'umma a Kano, Sheikh Abdulwahab Abdallah, ya bukaci babban Sufeton 'yan sanda ya bullo da wani sashe ko runduna domin gano yaran da aka sace.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment